KO KIRISTA SUNA DA RAGON LAYYA?

ID AL-KABIR

Dukan Musulmi suna da farin ciki lokacin Id Al-Kabir, wato Babban Salla, idan suke da ragon layya. Larabawa kuma suna kiran sallar nan Id Al-Adha, wato Sallar Hadaya. Kowa yana son lada. Mai gida za shi sayi dan rago mai girma. Ana fadi cewa ragon layya mai karfi zai taimake shi ketarewa, shi kai gidan aljanna. Idan mutum ba shi da abin da zai yanka, wani wuri za ka gani sai ya shafa jinin ragon liman a goshinsa, ko shi kai gida domin yaransa. Kowa yana son ladan ragon layya.

ANNABI IBRAHIM

A ina aka fara yanka dan ragon layya? Alkur'ani Suratus Saffat 37:99-111 ya ba da labarin annabi Ibrahim. Allah ya ce shi yanka dansa. Kuma Ibrahim ya yarda. Ana samun cikakken labarin abin da ya faru a Attaura Farawa 22:1-19.

[Yaron] ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, "Baba!"Sai ya ce, "Ga ni, dana."Ya ce, "Ga wuta, ga itace, amma ina ragon hadayar konawa?" Ibrahim ya ce, "Allah zai tanada wa kansa ragon hadayar konawa, ya dana.”...  Sai Ibrahim ya mika hannu ya dauki wukar don ya yanka dansa.  Amma mala'ikan Ubangiji ya yi kiransa daga sama, ya ce, "Ibrahim, Ibrahim!"Sai ya ce, "Ga ni." Ya ce, "Kada ka sa hannunka a kan saurayin, kada kuwa ka yi masa wani abu, gama yanzu na sani kai mai tsoron Allah ne, da yake ba ka ki ba da danka, tilonka, a gare ni ba." Ibrahim ya ta da idanunsa, ya duba, ga rago kuwa a bayansa, da kahoni a sarkafe cikin kurmi. Ibrahim kuwa ya tafi ya kamo ragon, ya mika shi hadayar konawa maimakon dansa. Sai Ibrahim ya sa wa wurin suna, "Ubangiji zai tanada," kamar yadda ake fada har yau, "A bisa kan dutsen Ubangiji, za a tanada." (Farawa 22:7-14).

IDIN KETAREWA

Yahudawa ba su yanka rago domin tunawa da Ibrahim ba.  Amma suna da Idin Ketarewa, wanda annabi Musa ya ba su.  A wannan sallah sai su yanka dan rago domin su tuna da ceto wanda Allah ya yi masu daren da ya fishe su daga gidan bauta a kasar Masar. A wancan dare Mala'ikan Mutuwa ya ketare kowane gida inda aka shafa jinin rago a dogaran kofar gida. Amma ya kashe dan fari a kowane gida inda babu jini. (Attaurat, Fitowa 12:1-14).

LAYYA CIKIN LINJILA

Mi ya sa Kirista ba su yankan ragon layya? Sai ka tuna da annabcin da Ibrahim ya fadi, cewa "Allah zai tanada wa kansa ragon hadayar konawa, ya danada kuma "Ubangiji zai tanada."  Allah ya ba Ibrahim dan rago abin fansa domin dansa. A cikin Linjila, annabi Yahaya Mai Baftisma ya ga Yesu, sai ya ce, "Kun ga, ga Dan Rago na Allah, mai dauke zunubin duniya!"  (Yahaya 1:29). Yesu ya ba da jininsa ran da ya mutu.  Aka rataye shi da kusoshi a hannu da kafa a bisa itacen gicciye.

Mi ya fi daraja? Ko jinin ragon layya, ko jinin mutum marar zunubi? Aka rubuta, "Ba mai yiwuwa ba ne jinin bijimai da na awaki ya dauki zunubi. Shi ya sa da Almasihu zai shigo duniya, sai ya ce, Hadaya da sadaka kam, ba ka so, amma kä tanadar mini jiki. Sa'an nan na ce, Ga ni, na zo in aikata nufinka, ya Allah, kamar yadda yake rubuce game da ni a Littafi.’ ”


Ta fadin haka Yesu Almasihu ya kawar da layya da sauran hadayu, ya ba da kansa. "Ta nufin nan ne aka tsarkake mu, ta wurin mika jikin Yesu Almasihu hadaya sau daya tak ba kari." (Linjila, Ibraniyawa 10:4-10).

HADAYA DAYA

"Almasihu da ya mika hadaya guda ta har abada domin kawar da zunubai, sai ya zauna dama da Allah. Gama ta hadaya guda kawai ya kammala wadanda aka tsarkake har abada. Sai ya kara da cewa, Ba kuma zan kara tunawa da zunubansu da laifofinsu ba. To, inda aka sami gafarar wadannan, ba sauran wata hadaya domin kawar da zunubi." (Ibraniyawa 10:12-18). Kirista ba su da bukatar yanka dan rago kowace shekara. Almasihu ya rigaya ya cika dukan abin da muke so. Ya mika kansa abin yanka domin shi fanshe mu. Ya mai da mu öan gida masu gädo a Sama. Dukan abin da yake da shi kuma, yana ba mu.

ID AL-QIAMA

Kirista ko'ina a cikin duniya sukan tuna da hadayar Yesu a lokacin salla wadda Larabawa suna ce da ita Id Al-Qiama. Français kuma suna kiranta Pâques. A sallar nan, Ran Juma'a Mai Tsarki Kirista suna tunawar da mutuwar Almasihu. Sa'an nan Ran Lahadi sai su yi murna da farin ciki saboda tashin Almasihu daga matattu. Wannan ya cika dukan ma'anar Sallar Layya da Idin Ketarewa.

LADA

Yesu Almasihu shi ne Dan Ragon Layya na gaske. Shi ne kuma Ragon Idin Ketarewa. Shi ne tanadin Allah wanda Ibrahim ya ambata. Jinin Yesu ya fanshe mu. Saboda jininsa muna samun lada mai yawa :

·      sulhu da Allah. "Allah ne ta wurin Almasihu yake sulhunta öan adam da shi kansa, ba ya kuwa lasafta laifofinsu a kansu" (2 Korantiyawa 5:19)

·      an yafe zunubanmu. “Ta gare shi [Yesu] ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah" (Afisawa 1:7).

·      wurin zama a gidan Aljanna. "Zan tafi in shirya muku wuri" (Yahaya 14:2).

·      lada domin aikinmu. Yesu ya ce, "Ga shi, ina zuwa da wuri, tare da sakamakon da zan yi wa kowa gwargwadon abin da ya yi" (Wahayin Yahaya 22:12).

TUBA DA BANGASKIYA

Yaya za mu sami ladan nan? Ta yaya za mu shafa jinin Almasihu a goshinmu? Hanya daya Allah ya yarda da ita. Wato, ta wurin tuba daga zunubi, da bangaskiya cikin Almasihu Yesu.

Tuba ta kumshi cewa kana bakin ciki saboda dukan laifofin da ka tađa yi, masu sađa dokar Allah. Da dukan zuciya sai ka juya ga barin wadannan zunubai. Daga yau za ka mika kanka ga tafiya cikin haske yadda Ubangiji Allah yake so.

Bangaskiya ta nufi yarda da Yesu Almasihu da mutuwarsa da tashinsa daga matattu. Kana roko shi zama Ubangijinka. Kuma ka yarda da barin dukan sauran addinai da malamai da bokaye da magunguna da layu. Za ka dogara ga jinin Yesu kadai domin samun ceto da dukan lada wadda ya kyauta wa masu binsa.

KARFIN RAGO

Shi ya sa Kirista ba su yankan ragon layya. Yesu shi ne ragon layya namu. Yana da karfi babu iyaka. Babu mutum ko mala'ika ko aljanni wanda yake da iko irin na Almasihu. Kowane mutum wanda ya dogara ga Yesu ya riga ya ketare mutuwa zuwa cikin rai madawwami, ba za a yi masa hukunci ba (Yahaya 5:24). Yesu ya mutu, ya koma ga rai, zai dawo domin mutanensa.

Ga wata addu'a. Idan da gaske kana son tuba, ka karđi Yesu Almasihu shi zama Ubangijinka, sai ka fadi wannan addu'a da zuciya daya ga Allah yanzu :

"Ya Allah, ga ni mai zunubi na zo. Na san laifofina suka ja mini hukuncin mutuwa. Ba ni da wani adalci wanda ya cancanta in zo a gabanka ba. Ya Allah, ina rokon gafarar zunubaina ta dalilin jinin Almasihu. Na gaskanta Yesu ya mutu, ya tashi da rai kuma a rana ta ukku. Yanzu na karđe shi, shi zama Ubangijina da Mai Cetona. Na gode saboda kai Mai Jinkai ne, Mai Alheri, Mai yawan gafara. Na kawo wannan addu'a a cikin sunan Yesu. Amin."

Allah ya sa ka yi imani da Yesu, shi kadai Mai Ceto ne. Amin.

            Idan ka yi addu'a domin ka zama mai bin Almasihu, bari wadannan shawarori su taimake ka cikin hanya zuwa Gidan Aljanna :